IQNA

23:56 - March 24, 2020
Lambar Labari: 3484652
Tehran (IQNA) cibiyar kula da harkokin kur’ani ta kasar Kuwait ta sanar da wani shiri na hardar kur’ani kyauta ta hanyar yanar gizo.

Shafin menafn ya bayar da rahoton cewa, Fahad aljanfawi shugaban cibiyar kula da harkokin kur’ani mai tsarki ta kasar Kuwait ya bayyana cewa, sun samar da wani shiri na musamman na horar da masu sha’awar hardar kur’ani ta hanyar yanar gizo.

Ya ce sun samar da wanann shirin ne sakamakon hutun da aka bayar a dukkanin makarantun kur’ani na kasar saboda kaucewa yaduwar cutar corona, domin matasa su yi amfani da wannan damar a zaman da suke yi a cikin gida wajen koyon hardar kur’ani.

Aljanfawi ya kara da cewa, wannan wata babbar dam ace ga matasa da ma duk masu son koyon hardar kur’ani cikin sauki, wadda za su iya yin amfani da manjar da aka saka kyauta ta hanayar yanar gizo.

 

3887028

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Kuwait ، horo na ، hardar kur’ani ، Fahad ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: