IQNA

23:50 - March 27, 2020
Lambar Labari: 3484664
Tehran (IQNA) kididdiga ta nuna cewa Amurka ce kan gaba a halin yanzu wajen yawan wadanda suka kam da cutar corona.

Kamfanin dillancin labara Anatoli ya bayar da rahoon cewa, bisa ga alkalumman da jami’ar Johns Hopkins ta kasar Aurka ta bayar, adadin wadanda suka kamu da cutar corona a Amurka a halin yanzu ya wuce na kasashen Italiya da China.

Jami’ar ta ce a halin yanzu Amurka da mutane dubu 85 da 653 da suka kamu da cutar corona, yayin da China take da dubu 81 da 782, sakuma Italiya take biye mata da dubu 80 da 589.

Ya zuwa ranar Ahamis mutane 1,178 ne cutar corona ta kashe a kasar Amurka.

Ita ma tashar CNN ta bayar da rahoton cewa, ranar Alhamis da ta gabata ita ce rana mafi muni, wadda corona ta kashe mutane 248 a kasar Amurka.

Ya zuwa yanzu dai mutane fiye da dubu 531 suka kamu da cutar corona a duniya, yayin da fiye da dubu 23 daga cikinsu suka rasa rayukansu.

 

 

3887625

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: rasa rayukansu ، cutar corona ، Amurka ، duniya ، Italiya ، kididdiga
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: