IQNA

Sanders Ya Janye Daga Takarar Shugabancin Amurka

23:56 - April 08, 2020
Lambar Labari: 3484692
Tehran (IQNA) Dan takaran fidda gwani na jam’iyyar demokrate sanata Bernie, Sanders, ya janya takararsa a zaben shugaban kasar Amurka a yau Laraba.

Hakan dai ya baiwa tsohon mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden, damar ya fafata da shugaba Tonald Trump a zaben Amurka na ranar 3 ga watan Nuwamba mai zuwa.

Nan gaba ne ake sa ran Bernie Sanders, mai shekaru 78 zai yi jawabi ga magoya bayansa ta kafar intanet.

Tunda farko tawagar kamfe ta Bernie Sanders, ta sanar da cewa kamfe ya kare amma yaki bai gama ba.

Tuni dai Joe Biden, ya bukaci aiki tare da kuma neman kuri’ar magoyan bayan Sanata Bernie Sanders.

 

 

3890317

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: dan takarar ، sugabancin ، Sanders ، janye ، daga takara ، Amurka ، yau
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha