IQNA

Rauhani: Har Yanzu Tsarin Instex Bai Yi Amfanin Da Ake Bukata Ba

23:54 - April 21, 2020
Lambar Labari: 3484730
Tehran (IQNA) Shugaba Rauhania zantawarsa da firai ministan Italiya ya bayana cewa, har yanzu sarin hada-hadar kudade na instex bai yi amfanin da ake bukata ba.

Firai ministan na kasar Italiya, Giuseppe Conte ya bayyan ahakan ne a wata tattaunawa ta yawar tarho da ya yi da shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani, ya kuma tabo batun fada a cutar corona, yana mai cewa; mun san yadda ku ke ji, kuma za mu yi maraba da duk wani aiki tare a tsakanin kasashen biyu domin fada da cutar.

Firai ministan na kasar Italiya ya kuma jaddada muhimmancin fadada alaka a tsakanin kasarsa da kuma Iran, musamman a fagen yarjejeniyar Nukiliya da kuma kafar musayar kudi ta ( Instex) da kasashen turai.

Conte ya kuma kara da cewa; wajibi ne a yi aiki da duk wata dama da ake da ita domin tabbatar da zaman lafiya a cikin yankin gabas ta tsakiya.

A nasa bangaren shugaba Rauhani ya bayyana cewa Iran tana fatan ganin wannan tsari ya yi aiki kamar yadda aka shirya, amma abin ban takaici har yanzu babu wani ci gaba na azi a gani da aka samu kan hakan.

Ya ce za su ci gaba da zura idi domin irin matakai na gaba da manyan kasashen tarayyar turai za su dauka kan wannan batu.

Haka nan kuma ya yi ishara da yadda wasu kasashe suka fara aiki da shirin, tare da bayyana cewa hakan mataki mai kyau.

3893019

 

captcha