Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Michelle Bachelet shugabar kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa, suna yin tir da duk wani mataki na cin zarafin jama’a da sunan yunkurin dakile corona.
Ta ce akwai rahotanni da dama da suke da su kan yadda wasu gwamnatoci suke yin amfani da karfi wajen takura jama’a, domin tilsta su zaman gida, daidai lokacin da wasu suna fita neman abin da za su ci ala tilas.
Bachelet ta ce dole ne gwamnatocin kasashe su yi la’akari da yanayin da mutanensu ke ciki kafin daukar kowane irin mataki, domin akwai masu bukatar tallafi kafin a killace su cikin gidajensu, saboda ba su tanadi abincin da za su ci da sauran abubuwan bukatar rayuwa ba.
Ta kara da cewa, akwai matakai na kiwon lafiya wadanda dole ne a dauke su domin kare lafiyar jama’a, amma bai kamata wajen daukar irin wadannan matakan a ci zarafin jama’a har ma wasu su rasa rayukansu ba, ta ce ya kamata ne a tausaya ma mutane da kuma tallafa musu a cikin irin wannan mawuyacin hali, musamman ma marassa karfi daga cikinsu.