IQNA

22:54 - May 07, 2020
Lambar Labari: 3484771
Tehran (IQNA) an saka karatun kur’ani mai tsarki a lokacin janazar shekh Muhammad Mahmud Tablawi a lokacin janazarsa.

Shafin yada labarai na yaum Sabi ya bayar da rahoton cewa,a yau aka gudanar da janazar babban malami makarancin kur’ani, wanda a gidansa an saka karatun Abdulbasit, amma daya daga cikin makwabta ya saka karatu da sautin mamacin.

Janazar Sheikh Tablawi ta samu halarta ‘yan uwa da danginsa da kuam mutanen gari da sauran al’ummar musulmi, gami da makaranta da mahardata kur’ani na yankin, an kuma gudanar da janazar ne a garinsa na haihuwa wato Alajuza da ke cikin gundumar Jizah.

Shekaran jiya ne Sheikh Tablawi ya rasu yana da shekaru 86 a duniya, bayan kwashe fiye da shekaru 60 yana hidima ga kur’ani.

3897204

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: sheikh Muhammad Tablawi ، Masar ، gundumar Jiza ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: