IQNA

An Nuna Tsohon Makullin Ka’abah A Dakin Kayan Tarihi Na Masar

23:47 - May 12, 2020
Lambar Labari: 3484788
Tehran (IQNA) an nuna wani tsohon makulli na dakin Ka’abah mai shekaru kusan dari bakawai a dakin ajiye kayan tarihi na kasar Masar.

Tashar Rusiia Today ta bayar da rahoton cewa, ma’aikatar yawon bude ido ta kasar Masar ta buje wani baje koli na kayayyakin tarihi, a babban dakin ajiye kayan tarihi na kasar, inda aka nuna wani tsohon makullin dakin Ka’abah a wurin.

Shugabar dakin kayan tarihin Masar Jihan Nabil ta bayyana cewa, wannan makulli tarihinsa na komawa ne zuwa ga lokacin sarki Sultan Ashraf Sha’aban.

A kan makullin an yi rubutun ayar kur’ani mai tsarki aya tafarko a suratul fathi.

Haka nan kuma akan makullin an rubuta sunan sarki Sultan Ashraf Sha’aban da kuma shekarar hijira ta 756, wato tsakanin shekara ta 1363 zuwa 1364 shekarar miladiyya.

Sarakunan Turkawa sun yi mulki a kan Masar da Sham a tsakanin shekarun 1250 zuwa 1517 miladiyya.

 

3898223

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tsohon makulli
captcha