IQNA

23:01 - May 18, 2020
Lambar Labari: 3484809
Tehran (IQNA) shugaban majalisar juyin juya hali a kasar Yemen Muhammad Ali Alhuthi ya bayyana cewa, ci gaba da killace kasar Yemen na daga cikin abubuwan da ke yin barazana ga rayuwar al’ummar kasar.

Tashar talabijin ta Almasirah ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da shugaban majalisar juyin juya hali a kasar Yemen Muhammad Ali Alhuthi ya saka a shafinsa na twitter, ya bayyana cewa bangarorin da ke da’awar cewa suna kare hakkokin al’ummar Yemen, dole ne su matsa lamba a kan masu yaki da al’ummar kasar ta Yemen, domin su kawo karshen killacewar da suke yi wa kasar.

Ya ci gaba da cewa, sakamakon killace kasar Yemen da masu yaki da kasar suka yi, a halin yanzu ba za a iya shigo da kayan kiwon lafiya a kasar ba, a daidai lokacin da ake fuskantar babban hadari na yiwuwar yaduwar cutar corona a kasar, a daidai lokacin da makiya al’ummar kasar suke ci gaba da kaddamar da hare-hare a kansu.

Daga karshe kuma ya bukaci al’ummar kasar da su kiyaye nasihohin jami’an kiwon lafiya, domin kaucewa kamuwa da cutar corona a kasar.

 

 

3899497

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar ، Yemen ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: