IQNA

22:42 - May 20, 2020
Lambar Labari: 3484818
Tehran (IQNAI Shugaban kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas Isma’ila Haniyya ya gargadi Isra’ila kan daukar duk wani mataki da ka iya kaiwa ga rusa masallacin Quds.

A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a yau a taron ranar Quds wanda ake kammalawa a yau a birnin Tehran ta hanyar hoton bidiyo na yanar gizo, Isma’ila Haniyya ya bayyana cewa, masallacin Quds na cikin gagarumin hadari, domin kuwa a kowane lokaci yahudawa za su iya rusa shi.

Ya ce kamar yadda dukkanin sauran yankunan Falastinawa suke cikin hadarin rusawa a kowane lokaci, masallacin Quds mai alfama shi ma bai kubuta ba, domin kuwa yanzu haka yahudawa sun rarake karkashin masallacin baki daya, inda a halin yanzu masalalcin yana akan rami ne, kuma zai iya zartaewa ya fada.

Haniyya ya kirayi al’ummomin musulmi na duniya baki daya da su zama cikin fadaka dangane da halin da alkiblarsu ta farko take ciki.

 

3900454

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: