Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, babban jami’I mai kula da harkokin siyasar wajen kungiyar tarayyar tarayyar turai Josep Borrell ya bayyana cewa, kasashen kungiyar tarayyar turai 25 daga cikin 27 sun cimma matsaya kan yin watsi da shirin da Isra’ila take da shi na mamaye sauran yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.
Ya ci gaba da cewa, kasantuwar wannan mataki na Isra’ila ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa, wannan yasa ala tilas kasahen tarayyar turai su yi watsi da hakan, kuma idan Isra’ila ta dage kan aiwatar da shirin nata na mamaye sauran yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan, akwai yiwuwar tarayyar turai ta kakaba mata takunkumi.
Gwamnatin kwarya-kwaryan cin gishin kai ta Falastinawa, tare da bangarori daban-daban a Falastinu, sun lale marhabin da matakin na kungiyar tarayyar turai, tare da kiran wasu daga cikin kasashen larabawa da su koyi da hakan.