IQNA

Maga Takardan Majalisar Dunkin Duniya Ya Isar da Sakon Taya Murnar Salla Ga Musulmi

23:48 - May 23, 2020
Lambar Labari: 3484828
Tehran (IQNA) babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterrres ya isar da sakon taya murnar salla ga dukkanin musulmi na duniya.

Shafin jaridar Khalij Times ya bayar da rahton cewa, a cikin wani jawabi da babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterrres ya yi kai tsaye ta hanyar yanar gizo, ga wakilan kasashe mambobi a kungiyar OIC, ya bayyana cewa; yana isar da sakonsa na taya murna ga dukkanin musulmi kan zagayowar wannan lokaci mai albarka na idin karamar salalla.

Ya ce hakika wannan karon lokacin salla ya zo ma musulmi cikin wani bahagon yanayi da ake fama da cutar corona, kamar yadda kuma a cikin irin wanann yanayi ne suka azumci watan Ramadan mai alfarma.

Ya kara da cewa wannan lokaci ne da dukkanin al’ummomin duniya za su hada karfi domin tunkarar wannan annoba domin ganin bayanta a duniya baki daya, wanda hakan ba zai tabbata sai an hada kai da kuma yin aiki tukuru.

Guterres ya ce yana fatan ibada da rahama da albarka da daukaka da ke cikin watan Ramadan, su zama abin da ke koyar da darasi wajen kawo fahimta da girmama juna tsakanin al’umma baki daya.

 

 

3900857

 

 

captcha