IQNA

Yahudawa Sun Kara Sabunta Dokar Hana Sheikh Sabri Shiga Masallacin Aqsa

23:36 - June 04, 2020
Lambar Labari: 3484861
Tehran (IQNA) gwamnatin Isra’ila ta kara tsawaita dokar hana babban limamamin masallacin Quds shiga cikin masallacin daga nan har zuwa watanni hudu.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da gwamnatin Isra’ila ta fitar a yau Alhamis, ta sanar da cewa ta kara dokar hana babban limamamin masallacin Quds shiga cikin masallacin daga nan har zuwa watanni hudu a nan gaba.

A nasa bangaren sheikh Sabri Ikramah babban limamin masallacin Aqsa ya bayyana cewa, babbar manufar wannan mataki ita ce rufe bakinsa, ta yadda yahudawa za su ci gaba da cin karensu babu babba a kan musulmi a birnin quds da kuma kan masallacin aqsa.

Shehin malamin ya ce wannan mataki ba zai hana shi yin magana ba, kuma hakan ba zai iya canja shi daga matsayinsa ba.

A cikin watan Janairun farkon wannan shekara ne gwamnatin Ira’la ta fitar da dokar hana sheikh Sabri Ikrama babban limamin masallacin quds shiga cikin masallacin, bisa hujjar cewa yana tunzura ja’a ma wajen sanya su yin bore ga dokokin Isra’ila a birnin Quds.

 

3903000

 

 

 

 

 

captcha