IQNA

Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Kur’ani Na Kasar Saudiyya Rasuwa

23:34 - June 06, 2020
Lambar Labari: 3484866
Tehran (IQNA) a jiya ne Allah ya yi wa Sheikh Mahmud Sukar babban malamin kur’ani na kasar Saudiyya rasuwa yana da shekaru 90.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, kwamitin mahardata kur’ani na kasar Saudiyya Maknun da ke da babban ofishi a birnin Riyad ya fitar da sanarwar rasuwar babban malamin kur’ani a kasar Sheikh Mahmud Sukar.

A cikin bayanin, kwamitin ya bayyana rashin malamin da cewa babban rashi ne ga dukkanin makaranta da mahardata kur’ani na kasar da ma na duniya baki daya.

Shehin malamin wanda dan asalin kasar Masar ne, ya rasu a brnin Akahira na kasar ta Masar a jiya, kamar yadda kuma malamai da masana suke ci gaba da mika sakon ta’aziyyar rasuwarsa.

An Haifi Sheikh Mahmud a garin Jiza na kasar Masar, sannan ya koma Saudiyya da zama tun yana dan shekaru 48 da haihuwa, inda ya zama daya daga cikin manyan malamai masu koyar da kur’ani a kasar, ya tarbiyantar da daruruwan makaranta da mahardata kur’ani

Haka nan kuma bai saka kansa cikin harkokin siyasa ba, an shedi shi da kyawawan halaye a cikin rayuwarsa.

 

3903103

 

 

 

 

captcha