IQNA

22:58 - June 07, 2020
Lambar Labari: 3484871
Tehran (IQNA) wasu daga cikin masu zanga-zanga a birnin New York suna baiwa musulmi kariya a lokacin da suke yin salla.

Shafin yada labarai na etro ya bayar da rahoton cewa,a jiya alokacin dubban mutane suke zanga-zangar adawa da nuna wariya  abirnin New York musulmi daga cikin masu zanga-zangar sun kabbara salla, sai kuma wadanda ba musulmi suka zagaye su domin hana ‘yan sanda su cutar da su.

A lokacin da musulmin suke cikin salla akasarin mutanen ad ba musulmi ba ne da suke cikin zanga-zangar sun yi musu kawanya, ta yadda wani ba zai iya cutar da su a lokacin da suke yin salla ba.

Wannan lamari dai ya dauki hankulan al’ummomin duniya, ta yadda hakan ya nuan wa duniya cewa a kowane lokaci al’umma za su iya haduwa su mara wa junansu baya domin cimma manufa ta ‘yan adamtaka, a daidai lokacin da kowannesu yake rike da addininsa ko akidarsa.

Daya daga cikin mutane da suka baiwa musulmin kariya wanda shi ba musulmi ba ne, ya ce hakkinsa ne ya kare musulmi domin su yi addininsu, domin hakan shi ne ‘yan adamtaka..

 

3903422

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ‘yan sanda ، zanga-zangar ، salla ، ‘yan adamtaka ، kawanya ، amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: