IQNA

23:05 - June 07, 2020
Lambar Labari: 3484873
Tehran (IQNA) Kungiyar Jihadul Islami mai fafutuka a Palestine ta bayar da sanarwar cewa, a yammacin jiya Asabar Allah ya yi wa tsohon babban sakarenta Dr. Abdullah Ramadan Shalah rasuwa.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, tsohon babban sakarenta Abdullah Ramadan Shalah ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya, wanda sakamakon hakan ne aka zabi mataimakinsa Ziyad Nakhala a shekara ta 2018 a matsayin babban sakataren kungiyar, wanda ya maye gurbinsa.

Tun a shekara ta dubu daya da dari tara da casa’in da biyar ne dai Ramadan Shalah yake a matsayin babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Jihadul Islami, wanda kuma an zabe shi ne bayan kisan shugaban kungiyar na farko Fathi Shiqaqi, wanda kungiyar leken asirin Isra’ila ta Mossad ta yi masa kisan gilla a cikin shekarar ta dubu daya da dari tara da casa’in da biyar.

A nata bangaren kasar Iran Ta Bayyana Alhininta Kan Rasuwar Tsohon Babban Sakataren Kungiyar Jihadul-Islami Ta Palasdinu

A sakon ta’aziyarsa kan rasuwar tsohon babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami Ramadan Abdullahi Shalah da ya rasu a jiya Asabar, Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana mamacin da cewa, Mutum ne mai kaunar ci gaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran a matsayinta na mai goyon bayan al’ummar Palasdinu da taimaka mata a gwagwarmayar neman ‘yanci.

Jawad Zarif ya bayyana tsananin bakin ciki da alhininsa kan rasuwar Dr Ramadan Abdullahi Shalah tsohon babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami ta Palasdinu bayan shafe tsawon shekaru yana gudanar da gwagwarmayar neman ‘yancin Palasdinawa da Masallacin Qudus mai alfarma.

Zarif ya kara da cewa: Marigayi Dr Ramadan mutum ne mai kishin kasa kuma dan gwagwarmaya da ya jure dukkanin wahalhalu da kuncin rayuwa tare da sadaukar da ransa ta hanyar fuskantar duk wani hatsari da barazana domin yakar bakar zaluncin gwamnatin Yahudawan Sahayoniyya ‘yan kaka gida.

Shugaban Falastinawa Mahmud Abbas ya bayyana rasuwar Abdullah Ramadan Shalah da cewa, al’ummar Falastinu ta rasa wani babban jigo shugaba mai sadaukarwa a kanta.

Kamar yadda sauran kungiyoyin Falastinawa da suka hada da kungiyar Hamas, suka bayyana rasuwarsa a matsayin wani babban rashi wada al’ummar Falastinu ta yi, tare da bayyana shi a matsayin daya daga cikin manyan jagororin al’ummar Falastinu da tarihi ba zai taba mantawa da shi da kuma gwagwarmayarsa ba.

A yammacin jiya Asabar ne tsohon babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Jihadul-Islami Dr Ramadan Abdullah Shalah ya rasu bayan fama da cutar ajali na tsawon lokaci, Allah ya jikansa da rahama tare da kyautata bayansa.

 

 

3903364

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: