IQNA

Mahukuntan Bahrain Sun Saki Nabil Rajab

23:53 - June 10, 2020
Lambar Labari: 3484879
Tehran (IQNA) a Bahrain an sallami, dan fafatukar nan Nabil Rajab bayan shafe shekaru hudu tsare a gidan kurkuku.

Lauyensa, Me Mohammed al-Jichi, ya ce an sallami Nabil Rajab, a jiya Talata, inda zai karasa sauren shekaru uku da suka rage masa ta wata hanya ta daban.

Rajab, na daga cikin ‘yan sananun ‘yan fafatuka a kasar ta Bahrain, dake nemau sauyi a salon mulkin kasar.
A shekara 2018, ne aka daure Nabil Rajab, bayan wallafa wasu sakwanni a shafinsa na twitter, dake sukan yakin da Saudiyya da kawayenta ciki har da kasar ta Bahrain, suka shelanta kan kasar Yemen, tare kuma da bankado yadda ake azabtar da jama’a a kasarsa ta Bahrain.

Tuni dai hukumar kare hakkin dan adam ta kasa da kasa, (FIDH), ta yaba da sallamar dan fafatukar Nabil Rajab.

 

3904018

 

 

captcha