IQNA

23:57 - June 10, 2020
Lambar Labari: 3484881
Tehran (IQNA) tarayyar turai ta yi watsi da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan.

A cikin bayanin da kungiyar tarayyar turai ta fitar kan shirin Isr’aila na mamaye sauran yankunan Falastinawa da ke gabar yammacin kogin Jordan, ta bayyana cewa ba za ta taba amincewa da hakan ba.

Bayanin kungiyar tarayyar turai ya ce abin da Isra’ila ke shirin yi, ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa, a kan haka kasashen tarayyar turai za su kalubalanci wannan shiri na Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa.

A yau ne ministan harkokin wajen kasar Jamus Heiko Maas zai isa birnin Tel Aviv domin ganawa da Netanyahu da wasu daga cikin jami’an gwamnatin yahudawan Isra’ila kan wannan batu.

A kwanakin baya dai tarayyar turai ta yi barazanar kakaba wa Isra’ila takunkumi, matukar dai ta aiwatar da shirin nata na mamaye yankunan Falastinawa yammacin kogin Jordan.

3904007

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: dukkanin dokoki ، ganawa ، mamaye ، yankuna ، hannun riga ، kalubalanci
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: