IQNA

Za A Yi Gyare-Gyare A Masallacin Manzo (SAW)

23:46 - June 11, 2020
Lambar Labari: 3484882
Tehran (IQNA) sarkin Saudiyya ya amince a gudanar da wasu gyare-gyare a masallacin manzo (SAW).

Shafin yada labarai na sabaq ya bayar da rahoton cewa, Abdulramad bin Abdulaziz Sudais shugaban kwamitin kula da haramin makka da madina ya bayyana cewa, sarkin Saudiyya ya amince a gudanar da wasu gyare-gyare a masallacin manzo (SAW) da ke Madina.

Ya ce ayyukan da za a gudanar sun hada da samar da tsari mai aiki da kansa na sauti da kuma wuta gami da na’urorin sanyaya wuri, kamar yadda za a fada wasu bangarorin masallacin, musamman wurin ajiye ababen hawa.

 

3904236

 

captcha