Gidan talabijin din na Uganda yana watsa hudubar ne sakamakon dakatar da gudanar da sallolin Juma’a da aka saboda dakile yaduwar cutar corona.
Sheikh Sulaiman Kasule ne yake gabatar da hudubar daga gidansa ana dauka ana watsawa domin amfanin musulmi.
Musulmin kasar Uganda na daga cikin musulmin da ake buga misali da sua bangarori daban-daban, da hakan ya hada da yadda suke rayuwa cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya tsakaninsu da ambiya addinin kirista.
Kasar Uganda da ke gabashin nahiyar Afirka, mafin yawan mutanenta mabiya addinin kirista ne, amma kuma suna zaman lafiya tare da musulmi, kamar yadda kuma suke girmama junansu.