IQNA

 Za A Gudanar Da Zama Kan Nuna wa Bakaken Fata Wariya A Amurka

22:53 - June 15, 2020
Lambar Labari: 3484897
Tehran (IQNA) Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya sanar da cewa, za a gudanar da zama domin yin bahasi kan cin zarafi da kuma nuna wa bakaken fata wariya da ake yi a Amurka.

Tashar France 25 ta bayar da rahoton cewa, a yau Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bayar da sanarwar cewa, bisa ga bukatar da kasashen Afirka suka gabatar, na neman majalisar dinkin duniya ta gudanar da zama kan cin zarafi da kuma nuna wa bakaken fata wariya a Amurka, dukkanin kasashe 46 mambobin kwamitin sun amince da wannan bukata ta kasashen Afirka.

Wannan kira dai ya zo ne sakamakon kisan da ‘yan sanda farar fata suka yi wa George Floyd bakar fata a jihar Minnisota da ke kasar Amurka, bayan haka kuma a cikin wannan makon, wani dan sanda farar fata ya sake harbe wani matashi bakar fata a birnin Atlanta da ke cikin Georgia  a kasar ta Amurka, inda ya kashe shi har lahira.

Wannan lamari dai ya kara harzuka jama’a matuka  a kasar ta Amurka, wanda hakan yasa babbar jami’ar ‘yan sanda ta birnin Atlanta yin murabus daga kan mukaminta, domin nuna takaici kan ta’asar da ‘yan sandan kasar ta Amurka suke tafkawa musamman a kan bakaken fata.

Kisan George Floyd dai ya yi sanadiyyar barkewar zanga-zanga a fadin kasar Amurka, inda jama’a suke nuna adawarsu da siyasar wariya da cin zarafin da ake yi wa bakaken fata a kasar, tare da yin kira a kan kare hakkokinsu kamar sauran ‘yan kasa.

Baya ga Amurka kasashen duniya da dama musamman an nahiyar turai, an gudanar da irin wannan zanga-zanga ta nuna adawa da wariya.

 

3905120

 

captcha