IQNA

Makarancin Kur’anin Da Yake Karatun Kur’ani A Karshen Rayuwarsa

23:49 - June 21, 2020
Lambar Labari: 3484912
Tehran (IQNA) sheikh Abduladi Abduljalil babban malamin kur’ani makaranci dan kasar Masar da ya rasu sakamakon kamuwa da corona.

Shafin yada labarai na almirsad ya bayar da rahoton cewa, wannan babban malamin kur’ani ya kasance har a karshen rayuwarsa yana karatun kur’ani, inda ya rasu yana karatun wasu ayoyi daga cikin surat Anbiya.

Sheikh Abduladi Abduljalil ya kasance a cikin wannan lokacin ne a lokacin da wasu suke daukarsa da bidiyo kamar yadda za a iya gani idan aka matsa hoton bidiyon.

3905898

 

 

 

captcha