IQNA

Sakon Hizbullah: Za Mu Iya Kai Hari Duk Inda Muke Bukata A Cikin Isra’ila

23:52 - June 21, 2020
Lambar Labari: 3484913
Tehran (IQNA) babban sakataren kungiyar Hizbulallah a cikin wani sako na sauti ya bayyana cewa, za su iya mayar da martani a duk inda suke bukata a cikin Isra’ila.

Shafin yada labarai na Hizbullah yasanar da cewa, a cikin sabon sakonsa, babban sakataren kungiyar Hizbulallah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, za su iya mayar da martani a duk inda suke bukata a cikin Isra’ila ba tare da wani shayi ba, matukar dai Isra’ila ta nemi yin wani shiahigi a kan kasa Lebanon.

Ya ce a halin yanzu kungiyar Hizbulah ba wai kawai za ta kai hari a cikin birnin Telaviv ba ne, za ta iya kai hari a duk inda take bukata a cikin Isra’ila.

Sayyid Nasrullah ya ce Isra’ila tana hankoron ganin ta kawo cikas ga karfin makaman Hizbullah, ya ce an riga an wuce wannan batun a halin yanzu.

 

 

3905860

 

Abubuwan Da Ya Shafa: hizbullah lebanon sayyid hassan nasrullah
captcha