IQNA

23:51 - June 23, 2020
Lambar Labari: 3484920
Tehran (IQNA) wasu gungun yahudawan sahyuniya sun kutsa kai a cikin masallacin aqsa mai alfarma.

Shafin yada labarai na Shihab News ya bayar da rahoton cewa, a yau Talata wasu gungun yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayi sun kutsa kai a cikin masallacin aqsa mai alfarma, tare da keta alfarmarsa.

Yahudawan wadanda yawansu ya kai fiye da dari daya, sun shiga cikin harbar masallacin mai afarma ne da nufin tsokanar musulmi, a daidai lokacin da wasu jami’an tsaron Isra’ila dauke da makamai suke bas u kariya.

Daruruwan matasa Falastinawa sun nemi shiga cikin masallacin domin kare alfarmarsa, amma jami’an ‘yan sandan yahudawan Isra’ila suka hana su shiga cikin masallacin da karfin tuwo.

 

3906567

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: