IQNA

Iran Ta Bayyana Matsayinta Kan Harbe-Harben Da Aka Yi Kan Iyakokinta Da Turkiyya

23:45 - June 24, 2020
Lambar Labari: 3484924
Tehran (IQNA) kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya yi Karin bayani akan fadan da aka yi a tsakanin sojojin Turkiya da kuma ‘yan ta’adda akan iyakar kasashen biyu.

Sayyid Abbas Musawi ya bayyana cewa; A bisa rahotannin da kafafen watsa labarun kasar Turkiya su ka watsa an yi taho mu gama a tsakanin sojojin Turkiyan da kuma ‘yan ta’adda akan iyakar Turkiya da Iran, wanda kuma a sanadiyyar hakan biyu daga cikin sojojin Turkiyan sun jikkata, kuma daya daga cikinsu ya kwanta dama.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya kara da cewa; A bisa rahoton da masu tsaron kan iyaka a gundumar Azaerbaijan ta yamma su ka bayar, wani harsashi ya shigo cikin iyakar kasar Iran, sai dai abin jin dadi babu wanda ya jikkata.

Bugu da kari kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce; Bangarori daban-daban na masu tsaron kan iyakar Iran suna ci gaba da gudanar da bincike akan abinda ya faru.

Musawi ya kuma bayyana takaicinsa da kuma jajantawa wadanda su ka cutu daga abinda ya faru, sannan kuma ya yi tir da kai da komawar ‘yan ta’adda a tsakanin iyakokin kasashen biyu da hakan kan jawo yin shahadar mutane a nan Iran da kuma Turkiya.

Musawi ya kuma ce; Mun sha bayyana cewa fada da ta’addanci wani nauyi ne da ya rataya akan duniya baki daya, don haka dole ne dukkanin kasashen su yi alkawalin aiwatar da shi, sai dai kuma matukar wasu kasashe na ci gaba da taimakawa ‘yan ta’adda za mu ci gaba da ganin afkuwar wadannan irin laifukan.

 

https://iqna.ir/fa/news/3906826

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :