IQNA

22:49 - June 27, 2020
Lambar Labari: 3484933
Tehran (IQNA) Kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta yi na’am da kudirin kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya da ke yin tir da take hakkokin musulmi a Myanmar.

A cikin wani bayani da ofishin babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta OIC ya fitar, ya yi lale marhabin da kudirin kwamitin kare hakkin bil adama na majlaisar duniya, wanda yake yin tir da Allawadai da muzgunawa musulmi ‘yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Baya ga haka kuma kungiyar ta OIC ta kirayi gwamnatin Mayanmar da ta yi aiki da hukuncin da kotun duniya ta yanke, wanda ya bukaci a kare hakkokin musulmi ‘yan kabilar Rohingya marassa rinjaye a kasar.

Kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya fiyar da kudiri wanda ya kirayi gwamnatin Myanmar da ta kawo karshen muzgunawa musulmi marassa rinjaye, tare da kamo jami’an tsaron kasar wadanda suka yi wa musulmi kisan kiyashi domin su fuskanci shari’a.

Ita ma a nata bangaren kotun duniya ta yanke hukunci makamancin hakan a ranar 23 ga watan Janairun farkon wannan shekara, bayan da ta samu cikakken rahoton kan irin kisan gillar da jami’an sojin gwamnatin Mayanmar gami da ‘yan addinin buda masu tsatsauran ra’ayi suka yi wa musulmi ‘yan kabilar Rohingya.

 

3906868

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kungiyar kasashen musulmi ، OIC ، Janairu ، musulmi ، kisan gilla
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: