IQNA

An Yi Na'am Da Matakin Kotu Na Neman Biyan 'Yan Uwa Musulmi Diyya A Najeriya

22:52 - June 30, 2020
Lambar Labari: 3484939
Tehran (IQNA) kungiyar kare hakkokin musulmi mai mazauni London a kasar Burtaniya ta yi na'a'am da matakin kotun tarayyar Najeriya na nemna a biya 'yan uwa musulmi diyya.

A jiya ne wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta umarci 'yan sandan Najeriya su biya 'yan uwa musulmi karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky Naira miliyan 15, saboda kisan da aka yi wa uku daga cikinsu yayin wani jerin gwano a Abuja.

Kotun dai ta gudanar da zamanta ne a Abuja babban birin kasar ta kuma umarci babban asibitin kasa ya bayar da gawawwakin uku a nan take ba tare da wani bata lokaci ba domin yi musu sutura.

Alkali mai shari'a Taiwo Taiwo, ya yanke hukuncin cewa, 'yan sanda za su biya Naira miliyan 5 ga kowane mamaci guda a matsayin diyyar kisan da aka yi masa.

Lamarin ya faru ne dai a lokacin da magoya bayan Harka Islamiyya suke gudanar da jerin gwanon lumana a birnin Abuja a ranar 22 ga watan Yulin 2019, domin yin kira da a saki Sheikh Ibrahim Zakzaky da mai dakinsa Malama Zinat da ake tsare da su, inda jami’an ‘yan sanda suka bude wutar bindiga a kan masu jerin gwanon, kuma majiyoyin Harka Islamiyya sun tabbatar da cewa mutane 9 ne ‘yan sanda suka kashe a lokacin.

Sai dai a nasu bangaren su ma ‘yan sanda sun zargi magoya bayan Harka Islamiyya da kashe musu mutum guda, amma Harka Islamiyya ta kore duk wani zargi na kisan wani jami’in tsaro a yayin jerin gwanon, inda ta tabbatar da cewa ba ta da masaniya kan hakan.

 

3907768

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ، ، ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* :