IQNA

Malaman Bahrain: Ayatollah Sistani Babban jigo Ne Da Ya Hada Kan Al’umma

23:51 - July 06, 2020
Lambar Labari: 3484956
Tehran (IQNA) Malaman addini a kasar Bahrain sun yi allawadai da cin zarafin malaman addini a kasar Iraki da jiridar kasar Saudiyya ta yi.

Malaman addini a kasar Bahrain sun fidda sanarwan yin allawadai da wulakanta malaman addini a kasar Iraki wacce wata jiridar kasar Saudiyya mai suna Assharqul Ausat ta yi.

A jiya Lahadi ce, malaman addini mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar Bahrain suka fidda wani bayani inda a cikinsa suka yi allawadai da jiridar Assharqul Ausat ta kasar Saudiya wacce a cikin bugunta na ranar Jumma’an da ta gabata ta wulakanta babban marja’in musulmi a kasar Iraqi, wato Ayatullah Ali Sistani.

Bayanin ya kara da cewa mutanen kasar Iraqi da saura musulmi ba za su taba manta da fatawar Ayatullahi Sistani ta jihadi a kan kungiyar Deash a shekara ta dubu biyu da sha hudu ba, wacce ta kai ga samar da mayaka wadanda suka kubutar da kasar Iraqi daga hannun kungiyoyin yan ta’adda, wadanda Amurka da kawayenta suka samar don rarraba kasar.

Wannan fatawar ta kare mutunci musulman kasar Iraqi, Shia da sunna, larabawa da ajamawa da kuma mabiya addinin Izadi wadanda suka wulakanta a hannun ‘yan ta’adda.

 

3908957

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: fatawa ، ayatollah sayyid ali sistani ، larabawa ، Saudiyya ، cin zarafi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha