IQNA

Littafi Kan Kyamar Musulunci A Siyasance A Kasar Amurka

23:10 - July 07, 2020
Lambar Labari: 3484960
Tehran (IQNA) an kaddamar da wani littafi da ke magana kan yadda batun nuna kyamar musulunci ya zama bangare na siyasa a kasar Amurka.

A zaman taron mane labarai da kamfanin dillancin labaran iqna ya jagoranta, an kaddamar da wani littafi da ke magana kan yadda batun nuna kyamar musulunci ya zama bangare na siyasa a kasar Amurka mai suna (Political Islamophobia at American Institutes: Battling the Power of Islamic Resistance) wanda Hakima Saqai Biriya ta rubuta.

Wannan littafi dai an rubuta shi ne a cikin shafuka 210, wanda cibiyar kare hakkin bil adama ta birnin London a kasar Burtaniya ta dauki nauyin buga shi.

Saeed Khan malami a jami’ar (Wayne State University) da ke jihar Michigan a kasar Amurka, wanda ya gabatar da jawabi kai tsaye ta hanyar hoton bidiyo yayin kaddamar da wannan littafi, ya bayyana cewa; hakika littafin ya kunshi muhimman lamurra da ya kamata a yi bayani kansu dangane da matsalar kyamar musulmi a Amurka.

Shi ma a nasa bangare Masud Shajare shugaban cibiyar kare hakkin bil adama ta birnin London a kasar Burtaniya, ya bayyana cewa abin da yake da matukar muhimmanci al’ummomin duniya musamman na musulmi su sani shi ne, shi batun kyamar musulmi a Amurka lamari ne da yake da alaka da siyasa.

Ita ma a nata bangaren wadda ta rubuta littafin ta bayyana cewa, akwai abubuwa da dama da suka karfafa gwiwarta wajen wannan rubuta, muhimmi daga ciki dai shi ne fadakarwa da kuma wayar da kan jama’a musamman musulmi domin su fahimi yadda lamurran suke a hakika.

3908966

 

captcha