IQNA

Wasikar Isma'ila Haniyya Shugaban Hamas Zuwa Ga Sayyid Hassan Nasrullah

23:45 - July 07, 2020
Lambar Labari: 3484962
Tehran (IQNA) Isma’ila Haniyya ya aike wa babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah da wata wasika

Shugaban kungiyar gwagwarmayr Falatinawa ta Hamas Isma’ila Haniyya ya aike wa babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasrullah da wata wasika, domin kara karfafa hadin gwiwa da ke tsakanin bangarorin biyu.

Shafin yada labarai na jaridar Al’ahad ya bayar da rahoton cewa, wasikar ta kunshi karin bayani kan matsayar Isra’ila ta neman aiwatar da shirinta na mamaye yankunan Falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan, da ma wasu batutuwan na daban.

Haka nan kuma Isma’il Haniyya ya jaddada muhimmanci ci gaba da kara dunkulewa wuri tsakanin dukkanin kungiyoyi masu fafutuka domin kare Falastinu da kuam wurare masu alfarma na musulmi da suke fuskantar barazana daga yahudawa a Falstinu, da hakan ya hada da masallacin quds.

Kungiyoyin Hamas da Hizbullah dai suna daga cikin kungiyoyin da suke gwagwarmaya domin fada da mamaye Isra’ila a cikin yankunan Falastinu da Lebanon, kamar yadda kuma suke da kyakkyawar alaka a dukkanin bangarori.

 

3909076

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha