IQNA

Cikar Shekaru 25 Da Kisan Kiyashin Srebrenica

An yi wa musulmi fiye da 8000 kisan kiyashi Wannan dai shi ne kisan kiyashi mafi muni wanda ya faru a nahiyar turai tun bayan yakin duniya na biyu. Shekaru 25 da faruwar wannan lamari a halin yanzu, kafin haka dai majalisar dinkin duniya ta shelanta birnin Srebrenica a matsayin tudun na tsira ga dukkan wadanda suka gudu suka shiga birnin, sannan ta jibge sojojin tabbatar da zaman lafiya a garin. Amma duk da haka yan kabilar sabiyawa sun shiga garin sannan a cikin sa'o'i arba’in da takwas sun kashe dubban musulman kasar Bosniya.