IQNA

Ana Jiran Bude Masallaci Na Uku Mafi Girma A Duniya A Aljeriya

18:03 - July 13, 2020
Lambar Labari: 3484981
Tehran (IQNA) Jama’a suna ci gaba da zura domin ganin an bude masallaci na uku mafi girma a duniya a kasar Aljeriya.

Shafin arabi 21 ya abyar da rahoton cewa, wannan masalalci dai shi ne masallaci na uku a duniya mafi girma, bayan masallacin Haramin Makka da kuma masallacin ma’aiki (SAW) da ke Madina.

Masallacin yana fadin mita dubu 180, kuma zai iya daukar masallata dubu 120 a lokaci guda, kamar yadda kuma yada wurin ajiye ababen hawa da zai iya daukar motoci dubu 6 a lokaci guda.

Haka nan kuma masallacin yana manyan dakuna taro guda biyu masu fadin mita dubu 16, daya yana da kujeru 1500 a cikinsa, daya kuma 300.

Haka nan kuma akwai dakin karatu mai fadin mita dubu 21 da 800, wanda yake da kujeru 2000 na zama a cikinsa.

Tun a cikin watan azumi da ya gabata ne dai aka shirya kan cewa za a bude wanann masallaci, amma saboda matsalar yaduwar cutar corona hakan yasa an dage lokacin bude shi har zuwa lokacin da aka samu saukin cutar.

Kasar Aljeriya dai tana daga cikin kasashen nahiyar Afirka da wanann cuta tafi yaduwa, wanda hakan yasa ala tilas aka dakatar da dukkanin harkoki a kasar, domin kaucewa yaduwar cutar.

Yanzu haka dai ana jiran mahukuntan kasar dangane da matakin da za su dauka kan bude masallacin, wanda dukkanin al’ummar kasar suke jiran wannan rana.

Ana Jiran Bude Masallaci Na Uku Mafi Girma A Duniya A Aljeriya

Ana Jiran Bude Masallaci Na Uku Mafi Girma A Duniya A Aljeriya

 

3910104

 

captcha