IQNA

Shugabannin Addinai A Myanmar: Zabuka Dama Ce Ta Sulhu Da Zaman Lafiya

18:40 - July 14, 2020
Lambar Labari: 3484984
Tehran (IQNA) shugabannin addinai a kasar Myanmar sun gudanar da zaman taro kan muhimmancin lokacin zabe domin kawo zaman lafiya da sulhu a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Herald Malasia ya bayar da rahoton cewa, a daidai lokacin da zabuka ke kara karatowa  a kasar Myamnar, jagororin addinai a kasar sun gudanar da zaman taro inda suka tattauna kan muhimmancin yin amfani da lokacin zabe domin kawo sulhu zaman lafiya mai dorewa.

Shugabannin addinan na Myanmar sun jaddada a wurin tarn nasu cewa, lokaci ya yi da za a karhsen duk wata gaba da nuna kin jinin wani jinsi a kasar saboda addininsa ko yarena ko kabilarsa, kasatuwar dukkanin mutane ‘yan adam ne ‘yan uwa juna, wadanda suke yin tarayya a cikin lamurra daban-daban.

Bisa ga wannan rahoton, shugabannin mabiya addinin kirista, da ‘yan Buda da kuma Hindus gami da musulmi, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin mabiya addinansu.

Gwamnatin kasar Myanmar dai na shan kakausar daga ko’ina cikin fadin duniya, kisan kiyashin da sojojin kasar suka yi wa muuslmi ‘yan kabilar Rohinya, tare kone garuruwansu da dukiyoyinsu , da kuma mayar da dubban daruruwa ‘yan gudun hijira.

 

3910466

 

captcha