Shafin yada labarai na kungiyar Ansarullah a kasar Yemen ya bayar da rahoton cewa, kwamitin mata a kasar Yemen ya fitar da wani bayani, inda ya yi kakkausar suka a kan majalisar dinkin duniya kan yadda ta yi shiru da bakinta kan kiyashin kiyashin da Saudiyya ke yi wa mata da kananan yara a kasar ta Yemen.
Wanann bayani na zuwa ne kwana daya bayan kisan gillar da jiragen yakin Saudiyya suka yi wa mata da kananan yara a jiya a lokacin bikin aure a lardin Jauf, inda suka kashe fararen hula 25 da tare da jikkata wasu da dama.
Kwamitin mata na kasar Yemen ya ce; yin shiru da majalisar dinkin duniya ta yi kan wannan lamari, shi kansa wulaknata al’ummar kasar Yemen ne.
Baynain nasu ya kara da cewa, hakan wata manuniya a kan cewa ko dai majalisar dinkin duniya ta zama wani bangare na masu goyon bayan wannan ta’addanci, ko kuma an riga an sayi lamirin manyan jami’anta da daloli.