IQNA

An Ragargaza Wani Sansanin ‘Yan Ta’adda A Borno

20:57 - July 17, 2020
Lambar Labari: 3484992
Tehran (IQNA) Ma’aikatar tsaron Najeriya ta sanar da cewa, mayakan sama na Najeriya sun samu nasarar ragargaza wani sansanin mayakan kungiyar Boko Haram a cikin jihar Borno.

Tashar TRT ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da kakakin ma’aikatar tsaron Najeriya Manja Janar John Enenche ya fitar, ya bayyana cewa; dakarun sama na Najeriya sun kaddamar da hari da jiragen yaki, inda suka wargaza wani sansanin na ‘yan ta’addan Boko Haram.

Sanarwar ta ce, an kai harin ne a sansanin ‘yan ta’addan da ke yankin Ngwuri Gana, inda bayan wargaza sansanin, an kuma kashe adadi mai yawa na mayakan ‘yan ta’addan.

Enenche ya ce an samu nasarar kai harin bayan samun bayanan sirri dangane maoyar ‘yan ta’addan, da kuma kai komon da suke yi a yankin.

Wannan dai na zuwa ne ‘yan kawanaki kadan bayan wani mummunan harin da mayakan kungiyar ta Boko Haram suka kaddamar a kan jami’an sojin ne a cikin jihar ta Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.

 

3910987

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: boko haram ، gabashin ، musamman ، mayakan ، ragargaza ، kadan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha