IQNA

An Fara Sassauta Dokar Hana Bude Masallatai A Rwanda

14:33 - July 21, 2020
Lambar Labari: 3485004
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Rwanda ta sanar da ta sassauta matakan hana bude masallatai a kasar.

Shafin yada labarai na tashar al-ikjbariyya ya bayar da rahoton cewa, a jiya gwamnatin kasar Rwanda ta sanar da ta sassauta matakan hana bude masallatai a kasar, inda za a ci gaba da bude masallatai bisa kaidoji da sharuddan da aka gindaya.

Daga cikin kaidojin dai har da bayar da tazara da kuma yin amfani da takunkumin rufe fuska, sannan kuma da yin amfani da kayan feshi na kashe kwayoyin cuta a cikin masallatan kowane lokacin kafin fara salla da bayan kammala salla.

Tun a cikin watan Yuni day a gabata ne dai mahukuntan kasar ta Rwanda suka fara daukar matakai na gudanar feshi da kuma kula da masallatai kafin a bayar da damar bude su domin yin salloli.

Kasar Rwanda dai tana daga cikin kasashen Afirka da ba a samu kamuwa da cutar sosai ba, inda mutane 1629 suka kamu, 5 daga cikinsu sun rasa rayukansu, wasu 838 kuma sun warke daga cutar.

3911748

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Rwanda ، cutar corona ، sassauta ، dokar hana bude ، masallatai ، mutane
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha