IQNA

Jami'an Tsaron Masar Sun Halaka 'Yan Ta'addan 18 A Sinai

23:55 - July 22, 2020
Lambar Labari: 3485009
Tehran (IQNA) jami'an tsaron kasar Masar sun samu nasarar halaka wani adadi na 'yan ta'adda a yankin Sinai.

Tashar France 24 ta bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron kasar Masar sun kaddamar da wasu hare-hare da sama da jiragen yaki a kan wata maboyar 'yan ta'addan takfiriyya a yankin Sinai.

Rahoton ya ce rundunar sojin kasar Masar ta tabbatar da cewa,a  yayin wannan farmaki an samu nasarar halaka 'yan ta'addan takfiriyyah 18, tare da jikkata wasu, yayin da sojoji biyu kuma suka rasa rayukansu.

An kai harin ne a garin Birul Abd da ke tazarar kilo mita 80 daga garin Alarish, inda 'yan ta'adda suka kai wani haria  cikin shekara ta 2017 a lokacin da ake gudanar da sallar juma'a, inda suka kashe masallata kimanin 300 a lokacin da suke salla.

3911891

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masar ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha