IQNA

Jamia’n Tsaron Tunisia Sun Damke Wasu ‘Yan Ta’adda

23:39 - July 23, 2020
Lambar Labari: 3485012
Tehran (IQNA) jami’an tsaron kasar Tunisia sun sanar da samun sarar damke wasu ‘yan ta’addan takfiriyya.

Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar da rahoton cewa, a wani samame da jami’an tsaron kasar Tunisia suka kai a kan wata maboyar  ‘yan ta’addan takfiriyya a kudancin kasar, sun cafke wasu daga cikinsu.

Ma’aikatar harkokin cikin gida a kasar ta Tunisia ta sanar ad cewa, yan ta’addan suna shirin kaddamar da wasu hare-hare a kan wasu yankuna na kasar.

An samu tarin makamai da kuma abubuwa mas fashewa a cikin mabiyar ‘yan ta’adan, gami nau’ion bindgogi daban-daban.

‘Yan ta’addan wadanda suke da alaka da kngiyar daesh, suna shirin kai haren-haren ansu ne a kan wasu wurare na bude ido da ke cikin kasar.

Baya ga Saudiyya, kasar Tunisia ita ce ta biyu wajen yawan ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi da suke kai hare-hare a cikin kasar Syria, inda a halin yanzu Turkiya ta kwaso wasunsu daga Syria zuwa Libya domin yaki da dakarn Haftar a kasar.

 

3911685

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: tunisia
captcha