IQNA

Cibiyar Musulunci Ta Burtaniya Ta Yada Wani Shiri Kan Shahadar Imam Baqer (AS)

18:58 - July 28, 2020
Lambar Labari: 3485030
Tehran (IQNA) cibiyar musulunci ta kasar Burtaniya ta yada wani shiri na musamman kan zagayowar lokacin shahadar Imam Baqer (AS) a cikin harsuna hudu.

Cibiyar ta fitar da wanann shiri ne ta hanyar yanar gizo da kuma kafofin zumunta na zamani, da nufin yada koyarwar Imam Baqer (AS) da kuma bayani a kansa da matsayinsa madaukaki.

An yada wannan shiri ne da kimanin karfe 19 na yammacin jiya Litinin 27 ga watan Yuli a cikin harsuna 4, Urdu, Larabci, Farisanci da turanci Ingilishi.

Za a iya samu wannan shirin da aka saka a cikin shafukan youtube da facebook ta hanayar wadannan adireshin:

YouTube: https://www.youtube.com/user/islamiccentre۱۹۹۸

FaceBook: https://www.facebook.com/IslamicCentreEngland

Haka ann kuma wadanda suke yin magana da Urdu da kuma Ingilishi, za su iya bin shirin a talabijin ta yanar gizo:

Ahlebait TV (SKY ۷۴۵) - https://ahlebaittv.net/watch-live

Hidayat TV (SKY ۷۳۳) - https://www.hidayat.tv/live

Haka nan kuma za a iya sauraren shirin ta hanayar sauti a yanar gizo ta wannan adireshi:

https://www.alqaimradio.com

 

3913044

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yammaci ، harsuna ، litinin ، Ingilishi ، hanyar ، zamani
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha