IQNA

Rauhani Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Idin Babbar Sallah Ga Shugabannin Kasashen Musulmi

22:56 - July 30, 2020
Lambar Labari: 3485037
Tehran (IQNA) shugaba Rauhani na Iran ya aike da sakon taya murnar idin babbar sallah ga shugabannin kasashen musulmi na duniya.

A cikin sakon nasa, shugaba Rauhani ya taya shugabannin kasashen musulmi murnar zagayowar wannan lokaci mai albarka na babbar salla ko kuma idin layya, tare da bayyana wannan lokaci da cewa wata babbar dama ce ga dukkanin musulmi da su kara hada kai su zama tsintsiya daya madaurinki daya, domin fuskantar manyan kalu bale da ke a gabansu.

Shugaba Rauhani ya bayyana idin bababr salla da cewa, wata rana daga cikin ranakun ubangiji, wadda Allah yasa mata albarka, a kan hakan ya yi fatan samun wannan albarka ga dukaknin al’ummar msuulmi, tare da yin fatan Allah ya kawo karshen cutar corona da ta addabi duniya baki daya albarkacin wannan idi da kuma ayyukan ibada da muminai suke yi a hajjin bana.

3913665

 

Abubuwan Da Ya Shafa: wata rana ، ranakun ، idin babbar salla ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha