IQNA

20:36 - August 08, 2020
Lambar Labari: 3485065
Tehran (IQNA) Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ya bayyana hatsarin da ya faru a tashar jirgin ruwa ta Beirut da cewa; Wani babban ibtila'i ne da ya aukawa al'ummar kasar Lebanon

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sayyid Hasrallah wanda ya gabatar da jawabi da marecen jiya Juma’a, ya bayyana hatsarin da ya faru a tashar jirgin ruwa ta Beirut da cewa; Wani babban ibtila'i ne,kuma da akwai sakamako na zamantakewa da kiwon lafiya da su ke biye da shi.

Sayyid Nasarallah ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda su ka rasa rayukansu, yana mai jaddada cewa hastarin ya shafi dukkanin mabiya addini da mazhabobi a kasar, haka nan kuma mutanen da su ka fito daga kowane banagre.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kara da cewa;tun sa’o’in farko na hatsarin, dukkanin kungiyoyin kasar su ka wuce gaba wajen gabatar da agaji da taimakon wadanda su ka jikkata, da kuma tsaftace tituna.

Har ila yau Sayyid Nasrallah ya ce; Kungiyar Hizbullah a shirye take ta gabatar da duk wani taimako ga gwamanti da kuma al’ummar Lebanon.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kore duk wata alaka a tsakanin Hizbullah da duk wani abu wanda yake a cikin tashar jirgin ruwan, a baya da kuma a yanzu.

Bugu da kari, Sayyid Nasrallah ya yi kira da a hukunta duk wadanda su ke da hannu wajen wasa da hankalin mutane na danganta abubuwan masu fashewa a tashar jirgin ruwan da kungiyar Hizbullah.

 

3915291

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: