IQNA

22:50 - August 11, 2020
Lambar Labari: 3485076
Tehran (IQNA) kungiyar kare hakkokin musulmi a Najeriya ta karyata zargin cewa tana karbar kudi daga kungiyar Boko Haram.

Shafin yada labarai na The Eagle Online ya bayar da rahoton cewa, kungiyar kare hakkokin musulmi a Najeriya ta Muslim Rights Concern ta  karyata zargin cewa tana karbar kudi dala dubu 200 daga kungiyar Boko Haram domin kawo matsaloli na tsaroa kasar.

Bayanin wanda shugaban kungiyar Ishaq Akintola ya karanta, ya bayyana zargi da cewa magana ce ta social Media maras tushe balantana asali da makama.

Ya ce kungiyarsu kowa ya san irin ayyukan da take gudanarwa a Najeriya, saboda haka idan har ma wanann zargi wanda ya yi shi bai sani ba, to al’ummar Najeriya sun sani cewa ba gaskiya ba ne.

Ya kara da cewa, a gina wannan zargin ne bisa wata magana da tsohon shugaban hukumar leken asiri na kasar mali San Louis Keita ya yi ne, inda yake cewa akwai wasu kungiyoy I da sunan kare hakkokin bil adama suna karbar kudi daga kungiyar Boko haram.

Wannan kungiya a halin yanzu dai it ace kungiyar ‘yan ta’adda mafi girma  a yammacin Nahiyar afirka, wadda ta aikata muggan laifuka na ta’addancia  kan bil adama a wasu kasashen yankin.

 

3915990

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Najeriya ، Muslim Rights Concern ، Ishaq Akintola ، gudanarwa ، gaskiya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: