Ayatollah Muhammad Ali Taskhiri Malami Ne Da Duniyar Musulmi Ba Za Ta manta Shi Ba
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin muslunci na Iran ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar Ayatollah Taskhiri.
A jiya Jagoran juyin juya halin muslunci na kasar Iran ya mika sakon ta’aziyyar rasuwar babban sakataren kwamitin koli na cibiyar kusanto da mazhabaobin muslunci na duniya Ayatollah Taskhiri, wanda Allah ya yi masa rasuwa yana da shekaru 76 a jiya.