Hujjarul Islam Saber Akbari jaddi wakilin jagora abirnin Moscow na kasar Rasha, ya bayyana cewa lamarin Ashura lamari ne na addini.

Malamin yace ko shakka babu lamarin Ashura lamari ne na addini wanda salihan bayi da suka tafi a kansa, kuma ci gaba ne na tafarkin annabwa (AS) domin kuwa Imam Hussain (AS) ya yi sadukarwa ne domin kare addinin nnabawa wanda shi ne addinin Allah na gaskiya.