IQNA

Hamas Ta Gargadi Isra’ila Kan ci gaba Da Killace Zirin Gaza

23:02 - August 24, 2020
Lambar Labari: 3485116
Tehran (IQNA) kungiyar Hamas ta gargadi gwamnatin yahudawan Isra’ila kan ci gaba da mamaye yankin zirin gaza.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, Fauzi Barhum kakakin kungiyar Hamas ya bayyana cewa, kungiyar tana gardadin gwamnatin yahudawan Isra’ila kan ci gaba da mamaye yankin zirin gaza da take yi.

Ya ci gaba da cewa, killace yankin da Isra’ila take yi yana  amatsayin yaki ne, domin kuwa kamar yadda take kashe mutane a lokacin yaki, to tana kashe mutane da wannan killacewar ta hanyar saka su cikin yunwa  da amtsaloli na rayuwa.

Haka nan kuma ya kirayi bangarori na kasa da kasa das u sauke nauyin day a rataya  akansu na ganin sun matsa lamba kan Isra’ila domin ta kawo karshen killace yankin zirin gaza da take yi.

Tun kimanin shekaru 14 ad suka gabata ne Isra’ila ta killace zirin gaza ta sama da kasa da kuma ruwa, tare da hana shigar da kayan abinci da sauran kayan bukatar rayuwa ga al’ummar yankin.

 

3918683

 

captcha