A yau ne aka gudanar da taron addu’ar kwanaki bakwai da rasuwar Ayatollah Taskhiri, inda fitaccen makarancin kur’ani dan kasar Iran Karim mansuri ya gabatar da tilawar kur’ani a wurin, tare da halartar manyan mutane daga ciki har da Abu Zar Ibrahimi Torkamani, shugaban hukumar yada al’adun musulunci.
Karim Mansuri dai yana daga cikin fitatattun makaranta kur’ani a duniya, wanda ya sha lashe gasar kur’ani ta duniya a lokacin kuruciyarsa, inda a halin yanzu yake koyarwa a cibiyoyin ilimi daban-daban na kasar Iran.