IQNA

22:42 - August 25, 2020
Lambar Labari: 3485119
Tehran (IQNA) Akalla mutane uku ne jami’an tsaro a birnin Kaduna na arewacin Najeriya suka kashe a lokacin da suka aukawa masu makokin Ashuran Imam Husain (a)a ranar Asabar.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, jami'an 'yan sanda a Kaduna dauke da makamai sun kai farmaki a wurin taron Ashura, inda suka kashe da kuma jikkata wasu daga cikin mahalarta taron.

Shafin yanar gizo na twitter mallakin harka Islamiyya na cewa Jami’an tsaro sun farwa taron Ashura na ‘yan shia a unguwar Hayin Bello insa suka bude wuta kansu, suka kashe mutane uku daga cikinsu a yayinda wasu da dama suka ji rauni.

Har’ila yau jami’an tsaron sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye kan masu zaman makokin. Yan shia mabiya Shiekh Ibrahim El-Zakzaky sun saba gudanar da juyayin Ashura a kowace shekara a Kaduna da wasu wurare. Amma tun lokacin da jami’an tsaro suka yi dirar mikiya a kan mabiyan shehin Malamin a shekara ta 2015 suke daukar irin wadannan wadannan matakan musamman ma a Kaduna.

3918824

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: