IQNA

Yahudawan Isra’ila Sun Ci Zarafin Wani Dattijo Musulmi Bafalastine

23:20 - September 02, 2020
Lambar Labari: 3485143
Tehran (IQNA) Sojojin yahudawan Isra’ila sun take wuyan wani dattijo farar hula musulmi bafalastine, a kauyen Shufa da ke kusa da garin Tolkaram.

Sojojin yahudawan Isra’ila sun sake maimaita abin da ‘yan sandan kasar Amurka suka yi  a kan George Floyd, inda suka take wuyan wani dattijo farar hula musulmi bafalastine, a kauyen Shufa da ke kusa da garin Tolkaram.

Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, yahudawan sun auka kan wasu gungun falastinawa ne da suke nuna rashin amincewa da wani shirin Isra’ila na kwace wani yanki daga cikin yankunansu a gundumar  Tolkaram.

Gwamnatin yahudawan Isra’ila na da shirin gina wani wurin shakatawar  yahudawa ‘yan share wuri zauna a kusa da kauyen, inda suka kwace wani yankin falastinawa mai fadin kilomita murabba’i 800.

Dattijon mai suna Khairi Hanun dan shekaru 65 da haihuwa, ya bayyana cewa sojojin yahudawan sun lakada masa duka a jikinsa, da nufin korarsa tare da sauran mutanen da yake tare da su, amma ya yi tsayin daka dauke da tutar Falastinu a hannunsa, inda daga karshe sojojin yahudawa suka kada shi a kasa, kuma danne wuyansa na tsawon wani dan lokaci.

Ya ce a lokacin da suka danne wuyansa jikinsa ya yi rauni ba zai iya motsawa, amma jamar da suke wurin ne suka kwace shi daga hannun yahudawan, wadanda suke yi masa barazanar harbe shi.

 

3920397

 

 

captcha