IQNA

22:42 - September 07, 2020
Lambar Labari: 3485159
Tehran (IQNA) musulmin kasar Afirka ta kudu na shirin kalubalantar hukuncin wata kotu da ya hana yada kiran salla  a wani masallacin musulmi.

Rahotanni sun bayyana cewa kotun birnin Durban ta hana saka kiran salla a wani masallaci da yake hade da wata cibiyar muslunci gami da makarantar Islamiyya a birnin.

Wannan hukunci ya zo bayan da wasu suka shigar da kara kan cewa, saka kiran salla a wannan masallaci ya sanya yanayin unguwar ya zama takar unguwar musulmi, kuma hakan yana damunsu.

Bayan shigar da wannan kara alkalin kotun ya yanke hukuncin cewa, a daina saka kiran salla ta yadda wanda ke wajen masallacin zai ji, sai dai a saka ta yada wadanda ke cikin masallacin ne kawai zai iya ji..

Lauyoyin wanann cibiya ta musulunci sun kalubalanci wannan hukunci, tare da bayyana cewa akwai dalilai da dama wadanda suka dogara da su a cikin kundin tsarin mulkin Afirka ta kudu da suka rusa wanann hukunci.

 

3921558

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: