Shafin yada labarai na akhirlahza-sd.com ya bayar da rahoton cewa, hukumomin jami'ar kur'ani ta kasar Sudan sun gudanar da zama, inda suka tattauna kan lokacin da ya dace a bude jami'ar, inda daga karshe sun bayyana ranar 18 ga watan Oktoba mai kamawa a mtsayin ranar komawa karatu.
A yayin zaman an jadda wajabcin ci gaba da koyar da dalibai da kuma yi musu bayani kan muhimman abubuwa da suka shafi darussansu ta hanyar yanar gizo.
Baya ga haka kuma an tattauna kan hanyoyin da za a bi wajen ganin an cike gibin karatun da aka samu na tsawon watanni kimanin bakawai.
3921712