IQNA

22:33 - September 09, 2020
Lambar Labari: 3485165
Tehran (IQNA) Manyan malaman addinin musulunci fiye da 200 ne suka bada fatawar haramcin kulla hulda da haramtacciyar kasar Isra’ila.

Shafin yada labaran arabi 21 ya bayyana cewa malaman sun fidda wannan fatawar ne a taron da suka gudanar ta yanar gizo a birnin Doha na kasar Qatar a ranar Lahadin da ta gabata.

Taron wanda kungiyar hadin kan malaman addinin musulunci ta shiya ya sami halattar manya-manyan malaman addini fiye da 200 daga kasashe daban-daban a duniya.

Labarin ya kara da cewa, abubuwan da suke faruwa a kasashen Larabawa a halin yanzu, na maida hulda da HKI, amincewa ne da mamayar wari mafi tsarki ga musulmi, sannan zai bawa HKI damar karasa mamayar da take yiwa Falasdinu da kuma korar sauran Falasdinawa daga kasarsu.

3922041

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: